Gwamnati na shirin fitar hatsin da ta adana domin daidaita farashin abinci a Najeriya.
Hassan Mamuda Ya'u 12 views

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin sakin hatsin da ta saya tare da adanawa a ƙarƙashin shirin Bankin Noma (Guaranteed Minimum Price Programme), domin sayar da su a kasuwa.
Matakin na da nufin ƙara yawan abincin da ake samu a kasuwa da kuma dakile tashin gwauron zabi na farashin kayan abinci, kamar yadda kafar DCL ta ruwaito.
Kazalika, gwamnati ta bayyana shirin raba buhunan takin zamani har miliyan uku cikin wata guda mai zuwa, a matsayin wani mataki na rage kuɗaɗen da manoma ke kashewa wajen noma tare da inganta wadatar abinci a faɗin ƙasar.
